Labarai
Gwamnatin tarayya ta kafa kwamatin bincike kan hatsarin jirgin ƙasa

Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamati na musamman da zai gudanar da bincike kan musabbabin hadarin jirgin kasan da ya auku a kan hanyar abuja zuwa kaduna a makon da mu ke ciki, Ministan Sufuri, Sanata Said Ahmed Alkali, ya kafa kwamiti domin samar da matakan da za su hana sake faruwar irin haka a nan gaba.
Ta cikin wata sanarwa da Darektar Yada Labarai da Bayanai, Janet McDickson Noah ta fitar ta rawaito cewa .
Kwamitin na karkashin jagorancin Musa O. Ibrahim daga daga Ma’aikatar Sufuri, tare da wasu kwararru daga hukumomin gwamnati, masana fasaha, jami’an jirgin kasa, ‘yan kasuwa, kungiyoyin farar hula, da kuma wakilan fasinjoji.
Sanata Alkali ya jaddada cewa manufar kafa wannan kwamiti ita ce gudanar da bincike mai zurfi tare da samar da shawarwari masu amfani, domin kare rayuka da kuma dawo da kwarin gwiwar jama’a ga harkar sufuri ta jirgin kasa.
You must be logged in to post a comment Login