Labarai
Gwamnatin Tarayya ta nemi taimakon tsofaffin sojoji domin dawo da tsaro a wasu yankuna

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin tura tsofaffin sojoji da suka yi ritaya domin kare yankunan da ba su da cikakken tsaro a kasar nan, a wani yunkuri na ƙarfafa tsaro da kuma farfaɗo da tattalin arziki a yankunan da rikice-rikice suka shafa.
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya ne ya bayyana hakan, in da ya ce an kafa kwamitin mutum 18 da zai jagoranci shirin kwato wadannan yankuna tare da sake inganta rawar da tsofaffin sojoji ke takawa.
Ministan ya bayyana cewa shirin zai rage dogaro da hare-haren soja kadai tare da amfani da ƙwarewar tsofaffin sojoji cikin tsaron al’umma da ayyukan ci gaba, musamman a wuraren da ikon gwamnati ya yi rauni.
Masu lura da al’amura na ganin cewa idan aka aiwatar da shirin yadda ya kamata, ayyukan laifuka da ta’addanci a yankunan da ba a kula da su ba za su ragu, yayin da tsaron al’umma zai ƙaru kuma tsofaffin sojoji za su samu damar ci gaba da ba da gudummawa ga zaman lafiyar ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login