Connect with us

Kasuwanci

Gwamnatin tarayya ta rufe kamfanonin samar da Taki guda 4 a Kano

Published

on

Gwamnatin tarayya ƙarƙashin ma’aikatar albarkatun Noma ta tarayya ta rufe wasu kamfanonin samar da taki gida 4 a Kano.

An rufe kamfanonin ne sakamakon kama su da laifin samar da taki mara inganci, kuma ba tare da sahalewar hukuma ba.

Da yake rufe kamfanonin babban jami’in da ke kula da samar da taki na ƙasa Okey Sunday ya ce ba za su lamunci irin waɗannan kamfanoni ba.

Sunday wanda yake jagorantar tawaga ta musamman da ta gudanar da zagayen kwanaki biyu a kamfanonin sarrafa taki ba Kano ya ce “Matukar muka zuba ido aka ci gaba da samar da gurɓataccen taki ga al’umma ba mu yi aikin da ya kamata ba”.

Kamfanonin Takin da aka rufe sun haɗar da : Kamfanonin Albarka Agro and Chemical Fertilizer da Nagarta Fertilizer a garin Zara da ke ƙaramar hukumar Kumbotso.

Sai kuma kamfanin SAMU a Jido da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu da kuma wasu shagunan sarrafa Takin a garin Getso da ke ƙaramar hukumar Gwarzo.

Wakilin Freedom Radio Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, tawagar da dakatar da kamfanonin ne bisa rashin lasisin aiki da kuma samar da Taki mara inganci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!