Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaftar muhalli: Hassana Bala ta zama gwarzuwar ma’aikatan shara a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ayyana Hassana Bala a matsayin gwarzuwar shekara a cikin ma’aikatan da suke sharar titi.

Karramawar na zuwa ne ta hannun ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano a ranar Asabar.

Tun da fari dai abokan aikin Hassana sun tabbatarwa da tawagar tsaftar muhalli cewa ita jajirtacciyar ma’aikaciya ce.

Sun kuma shaida cewa Hassana na fitowa aiki tsakar dare ko da kuwa ana tsaka da yin ruwan sama.

Har ma suka ce ta kan dauki sharar da kanta ta je ya zubar.

Wannan ne ya Sanya kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim ya ayyana ta a matsayin gwarzuwar shekara a ma’aikatan shara na Kano, inda a nan take ya Bata kyautar naira dubu 10.

Ya kuma yaba bisa kwazonta da kuma tabbatar da cewa duk inda be aka ware mata ta share yana tsaftace a koda yaushe.

A cewarsa “irin wadannan ma’aikatan muke bukata masu kishi da kwazo, a don haka za mu kirawo ta mu bata lambar yabo don karramata”.

Hassana Bala dattijuwa ce, mai kimanin shekaru sama da hamsin wadda ke aikin sharar titunan Kano, kuma ta samu karramawar ne yayin da ake duban tsaftar muhalli na karshen watan Yuli.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!