Labarai
Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranar fara hukunta masu shigo wa ba bisa ka’ida ba

Gwamnatin tarayya ta sanya ranar 1 ga watan Agustan bana a matsayin wa’adin fara bayar da tsattsauran hukunci ga baki ‘yan kasashen waje da suka wuce gona da iri.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai, bayan kammala taron wayar da kan masu ruwa da tsaki kan manyan sabbin fasahohin da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya ta yi kan tafiye-tafiyen fasinja na kasa da kasa, a shalkwatar Hukumar da ke Abuja.
Ya kuma ce, tsarin biza ta zamani da aka kaddamar kwanan nan ya aiwatar da aikace-aikace sama da 14,000 a cikin makonni shida na farko da fara wa.
Ministan ya kuma shaida wa mambobin jami’an Ofishin jakadancin kasashen ketare cewa, su gaya wa jama’ar irin matakin da za’a rika dauka da zarar an karya dokar kasa.
You must be logged in to post a comment Login