Labarai
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da ceto ɗalibai 100 na St. Mary’s

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da ceto ɗalibai 100 daga cikin mutane 315 da ’yan bindiga suka sace a Makarantar St. Mary’s da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara a Jihar Neja.
A rana ta farko bayan harin, yara 50 sun yi nasarar tserewa tare da komawa hannun iyalansu,inda suka rage saura su 265 kafin wannan sabon cigaba na ceto wasu daga cikinsu.
Idan za’a iya tunawa ’Yan bindigar sun kai farmakin ne a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, tare da mamaye makarantar suka kuma tafi da mutum 315 da suka haɗa da ɗalibai 303 da malamai 12.
Gwamnatin jihar dai ta bayyana cewa kafin aukuwar lamarin ta samu sahihan bayanan sirri game da yiwuwar tashin hankula a sassan Neja ta Arewa, saboda haka ta dakatar da ayyukan gine-gine tare da rufe makarantu masu kwana a yankunan da abin ya shafa.
You must be logged in to post a comment Login