Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya zata kafa kwamitin kolin da zai bada shawarwarin kirkire-kirkire fasahar zamani

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce zata kafa kwamitin koli da zai riga bata shawarwarin kan kirkire-kirkere fasahar zamani, don inganta bangare a fadin kasar nan.

Mataimakin shugaban kasa Ferfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai, bayan da ya kai ziyara gani da ido a cibiyoyin kere-keren fasaha daban-daban da ke a jihar Legas.

Ferfesa Osinbajo ya kuma ce, a halin yanzu akwai tsare-tsare da dama da gwamnatin tarayya ta bujiro da su a bangaren fasaha inda matasan kasar nan da dama za su amfana.

Ya Kara da cewa, bisa la’akari da abubuwan da ya gani a cibiyoyin fasaha a jihar Legas, kasar zata bi sahun manyan kasashen duniya da ke kere-kere a fadin duniya.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,926 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!