Labarai
Atiku Abubakar ya daukaka kara
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP da jam’iyyar PDP sun daukaka kara a kotun koli suna kalubalentar nasarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a a babban zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 23 ga watan Fabarairun da ya gabata.
Atiku Abubakar da jami’iyyar PDP sun shigar da karar ne bayan da kotun sauraran kararrakin zabe ta yi watsi da karar da ya shigar gaban ta wanda aka kwashe awanni Tara ana yi kafin a yanke hukuncin, yayin da kotun ta sake jadada cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya samu nasara a yayin zaben.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da babban lauya a cikin kunshin lauyoyin dake kare Atiku Abubakar Mike Ozekhome ya fitar cewa kotun sauraran kararrakin zaben tayi kuskure ko kuma ba tai dai-dai ba a hukuncin da ta yanke kan babban zaben shugaban kasar.
Haka zalika dan takarar shugaban kasar Atiku Abubakar da kuma jam’iyyar PDP sun shigar da karar ne kan hujoji 5.