Connect with us

Labarai

‘Yan bindiga sun sace dan kasuwa a Sokoto

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sun sace tare da yin garkuwa da wani dan kasuwa Alhaji Tukur Sabaru a jihar Sokoto.

Rahotanni sun bayyana cewar, an sace Alhaji Tukur Sabaru a gidan sa dake yankin karamar hukumar Dange-Shuni a jihar Sokoto.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar ta Sokoto ASP Muhammad Abubakar Sadiq ya tabbatar da sace dan kasuwar yana mai cewar,a daren jiya ne suka sami kiran gaggawa daga ofishin ‘yan sanda na Kwannawa suna  sheda masa an sace dan kasuwar yayin da kuma aka yi awan gaba da shi.

ASP Muhammad Abubakar Sadiq ya kara da cewar rahotanni da suka tattara ya nuna cewar ‘yan bindigar sun yi ta harbin mai kan-uwa-da-wabi  yayin da harbin ya sami mai dakin Alhaji Tukur Sabarun a hannun ta.

Kakakin rundunar yace tuni aka garzaya da wadanda suka sami raunika a asibiti don kulawar gaggawa.

Muhammad Abubakar Sadiq ya baiwa alummar tabbacin rundunar na kokarin kama wadanda suka aikata wannan laifin don fuskatar hukunci.

Kawo yanzu ‘yan bindigar basu kira iyalan dan kasuwar ba don neman kudin fansa ko kuma sakin sa.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,603 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!