Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Zamfara za ta dawo da harkokin sadarwa a Gusau

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya amince da dawo da harkokin sadarwa a Gusau babban birnin jihar daga yau Juma’a.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zailani Bappa ya fitar a yau.

Sanarwar ta bayyana cewa, dawo da harkokin sadarwa a babban birnin jihar, zai taimakawa ma’aikatun gwamnati da masu zaman kan su wajen gudanar da ayyukan su na yau da kullum.

A cewar sanarwar, gwamna Matawalle ya alkawarta ɗaukan matakin da ya kamata don kare al’ummar jihar, kuma nan ba da jimawa ba zai sanar da mataki na gaba.

Kazalika sanarwar ta bayyana cewa, dawo da harkokin sadarwar ya biyo bayan nasarar yaƙi da ayyukan tsaro a babban birnin na Gusau.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!