Labarai
Gwanatin Najeriya ta kafa kwamitin da zai kula da hannayen jari
Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da kwamitin gudanarwar Hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta kasa a jiya Litinin.
Babban sakatare a ma’aikatar kudi Alhaji Mahmud Isa Dutse ne ya kaddamar da kwamitin gudnarwar mai kunshe da mutum tara yana kuma karkashin jagorancin Mr Olufemi Lijadu.
Kaddamar da kwamitin gudanarwar na zuwa ne shekaru hudu bayan rushe tsohwar kwamitin gudanarwa wanda ke karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi.
Da ya ke gabatar da jawabi babban sakatare a ma’aikatar kudi Alhaji Mahmud Isa Dutse, ya bukaci sabbin ‘yan kwamitin gudanarwar Hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta Najeriya da su gudanar da aikin su bisa gaskiya da adalci.
Alhaji Mahmud Isa Dutse ya kuma ce gwamnatin za ta ci gaba da sa ido don ganin cewa lamura na gudana kamar yadda ya kamata a kasuwar hannayen jari ta Najeruya.