Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An kaddamar da kwamitin bincike kan zargin badakalar kudi a hukumar NPA – Amaechi

Published

on

Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya kaddamar da kwamitin da zai binciki zargin badakalar kudi da ake yi wa hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta kasa NPA karkashin Hadiza Bala Usman.

Yayain kaddamarwar, Rotimi Amaechi ya bukaci kwamitin da ya gudanar da aikinsa cikin gaskiya da adalci.

Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Auwalu Sulaiman, daraktan kula da harkokin teku, wanda zai samu tallafin Mr Ben Omogo, daraktan tsare-tsare da ci gaba a ma’aikatar.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar wakilai ke kira ga EFCC da ta bincika lamarin, kamar yadda shugaban marasa rinjaye na majalisar Ndudi Elumelu ya bukata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!