Labaran Kano
Gwmnatin Kano ta ankarar da masu saida magugunan dabbobi
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci masu sana’ar sayar da magungunan dabbobi ta jiha da su maida hankali wajen gudanar da kasuwancin su bisa doka da oda.
Babban sakataren ma’aikatar gona na jihar Kano Alhaji Adamu Abdu Faragai ne ya ja hankalin ‘yan kungiyar masu sayar da magungunan dabbobi na jiha, yayin wata ziyara da suka kawo masa ziyara ofishinsa.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran ma’aikatar gona, Hafizu Lawan ya sanyawa hannu.
Alhaji Adamu Abdu Faragai ya ce bin doka da oda na daga cikin hanyoyin da za su basu damar gudanar da kasuwancin su cikin walwala da kuma kawo ingantuwar tattalin arziki.
Hukumomin kiwon lafiya na yin dukkanin mai yuwa kan cutar lassa- Sarkin Kano
Kano: Hukumar KAROTA ta kai sumame wajen boye magunguna
Wasu magungunan kwari da manoma ke amfani da su na da illa ga lafiyar dan Adam
Babban sakataren ma’aikatar gona ya bayyana goyon bayan ma’aikatar wajen kawo ci gaba a tsarin kasuwancin su don bunkasar tattalin arziki.
Da yake bayani, jagoran ‘yan kasuwar da suka kawo ziyarar Alhaji Garba Abdullahi Dawakin Kudu yace makasudin ziyarar ta su shine don neman goyon ma’aikatar tare da gabatar da kasuwancin su cikin ka’idar doka da hukumomin suka shimfida.
Alhaji Garba Abdullahi Dawakin Kudu ya kuma nemi ma’aikatar gona ta jihar Kano da ta tallafa musu wajen ganin kasuwancinsu ya bunkasa.
You must be logged in to post a comment Login