Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Haɗarin jirgin ƙasa: Direban adaidaita sahun da lamarin ya rutsa da shi ya rasu

Published

on

Direban Adaidaita sahun nan Abdulwahab Jibrin da hatsarin jirgin ƙasa ya rutsa da shi a nan Kano ya rasa ransa.

Abdulwahab ɗan asalin unguwar Ƙofar Nassarawa mazaunin unguwar Hotoro ya rasu a jiya Litinin, an kuma yi jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tsara.

Wani makusancin marigayin Muhammad Bello Sulaiman Ƙofar Nassarawa ya yiwa wakilinmu Freedom Radio Ahmad Hamisu Gwale ƙarin bayani inda ya ce “Marigayin ba shi da aure matashi kuma ADAIDAITA sahun ba nasa bane, na abokin sa ne yake haya da shi”.

Har ma ya ce “Lokacin da hatsarin ya faru ta tafi zuwa yin murnar ɗaurin auren wani abokinsa ne sai ya gamu da ajalinsa”.

Idan zaku iya tunawa a ranar Lahadi ne wani jirgin ƙasa da ya taso daga Legas zuwa nan Kano, ya yi sanadiyyar murƙushe motar dakon siminti tare da baburin Adaidaita sahu a kan titin Obasanjo da ke nan Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!