Labarai
Har yanzu akwai sama da biliyan 7 da ba biya ma’aikatan wucin gadi ba – Festus Kiyamo
Gwamnatin tarayya ta ce har yanzu akwai kimanin Naira biliyan 7 da miliyan 3 da ba a rabawa waɗanda suka ci gajiyar shirinta na samar da ayyukan yi na musamman guda 774,000 da ta tsara ba.
Ƙaramin ministan ƙwadago da samar da aiki Festus Keyamo ne ya bayyana haka a yayin zaman kare kasafin kuɗi a gaban kwamitin harkokin kuɗi na majalisar dattawa kan ayyukan ƙwadago a Abuja.
Ya ce, shirin wanda aka samar da shi ƙarƙashin cibiyar samar da ayyukan yi ta kasa, ya ɗauki nauyin bai wa ƴan Najeriya 774,000 aiki a fadin kasar nan domin gudanar ayyukan gwamnati na tsawon watanni uku.
Keyamo ya alaƙanta jinkiri ga matsalolin banki, amma ya yi alƙawarin cewa za a raba sauran kuɗaɗen kafin ƙarshen watan Disambar 2021.
Ministan ya ce, ma’aikatar ta buɗe hanyar da wadanda suka ci gajiyar shirin za su iya amfani da kowane banki a yankinsu, musamman ga waɗanda ba a biya su albashin ba kusan shekara ɗaya.
You must be logged in to post a comment Login