Kasuwanci
An cimma matsaya tsakanin gwamnati da kamfanin Twitter
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2021/11/Buhari-and-Twitter.jpg)
Gwamnatin tarayya ta ce, kamfanin Twitter ya amince da dukkanin sharuɗɗan da ta gindaya masa gabanin ci gaba da gudanar da ayyukan sa a Najeriya.
Ƙaramin ministan ƙwadago da samar da aikin yi Festus Keyamo ne ya sanar da hakan, a wata hira da gidan Talabijin na Channels ya yi da shi a ranar Lahadi.
Festu Keyamo wanda guda ne daga cikin mambobin kwamitin da gwamnati ta samar da zai nazarci ayyukan kamfanin na Twitter tun a ranar 4 ga watan Yunin shekarar da muke ciki.
A cewar Festus Keyamo, kwamitin na samun ci gaba a tattaunawar da yake yi da kamfanin na ganin an daidaita.
Idan za a iya tunawa an dakatar da kafanin ne sakamakon goge wani rubutu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a shafin sa.
Solacebace:
You must be logged in to post a comment Login