Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Har yanzu ana ci gaba bayar da bashin noma – RIFAN

Published

on

Kungiyar masu noman shinkafa ta kasa RIFAN ta ce har yanzu ana ci gaba da bai wa manoma bashin kayan aikin noman shinkafa ga wadanda suka nemi a basu bashin a dukkannin kananan hukumomin Kano arba’in da hudu.

Shugaban kungiyar ta RIFAN reshen karamar hukumar Rogo Alhaji Yusuf Dan Haya Gwangwan ne ya bayyana hakan lokacin da ya ake bai wa wadanda suka nemi bashin kayan aikin noman na shinkafa a karamar hukumar Kiru.

Yusuf Dan Haya Gwangwan ya kara da cewa tsaikon da suke fuskanta wajen ci gaba da aikin bai wa wadanda suka nemi rance yana da alaka ne da tantance wadanda suka nemi bashin.

Wasu daga cikin manoman daga kananan hukumomin Madobi da Rogo wadanda aka kammala aikin tantance su, sun nuna farin cikinsu a yayin rabon.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito cewa, ya zuwa yanzu an tantance manoman shinkafa na kananan hukumomin Madobi da Bebeji da kuma Rogo.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!