Labarai
Harajin kashi 15 da shugaba Trump ya kakaba wa ƙasashen duniya ya fara aiki

Sabon harajin kashi 15 cikin 100 da shugaban Amurka, Donald Trump ya laftawa dukan ƙasashen duniya ya fara aiki.
Shugaban ya sanar da matakin ne, bayan hukuncin da Kotun kolin kasar ta yanke ranar Juma’a, inda ta ayyana haraje harajen da yake sanyawa a matsayin wadanda suka saba wa doka.
A yanzu dai sabon harajin na kaso 15 da ya sanya karkashin wata dokar ta daban ya shafi hatta kawayen Amurka, ciki har da Birtaniya da Australia.
To amma duk da haka zai kasance wani sauki ga wasu kasashen kamar China da Brazil wadanda ke takun sakar tattalin arziki da gwamnatin Trump.
Hukuncin da kotun kolin ta yanke ya janyo dakatar da yarjejeniyoyi da dama na cinikayyar kasa da kasa da aka amince da su ko kuma ake kokarin cimma matsaya kansu da Amurkar.
You must be logged in to post a comment Login