Labarai
Hisbah na shirin kara inganta ayyukanta a kananan hukumomi
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce nan bada jimawa ba zata inganta ayyukan dakarun ta dake kananan hukumomin jihar nan 44.
Babban Daraktan Hukumar Hisbah na jiha Dakta Aliyu Musa Aliyu ne ya bayyana hakan kasancewar hukumar ta Hisbah a yanzu haka na kokarin ganin an kar ingantawa tare da sake yin nazari kan yadda take gudanar da ayyukan ta a daukacin kananan hukumomin ta.
Dakta Aliyu ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar kundin rahoton yadda aka gudanar da aikin tantance dakarun Hisbah na kananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Haka kuma ya bayyana rashin jin dadinsa game da yadda ayyukan Hisbah ke gudana a wasu daga cikin kananan hukumomi, inda ya ci alwashin cewa, za su hada kai da ma’aikatar kula da kananan hukumomi da kuma shugabannin kananan hukumomin domin ganin cewa al’amura sun dai-daita tun daga yadda za’a bi wajen dauka ko maye gurbin dakatar da duk wani dan Hisbah da za’a yi.idan yayi laifi ko kuma ya bar aiki.
Jami’an Hisba sun cafke mata masu zaman kansu
Yadda hukumar Hisbah ta sauke ‘yan kwamitin gudanarwarta
Hisbah ta cafke matashi kan yunkurin haikewa budurwar abokinsa
Har Ila yau, Dr.Aliyu Musa ya yabawa kwamitin bisa yadda suka gudanar da ayyukansu tare da tabbatar musu da cewa za su ci gaba da tuntubar su a duk lokacin da wani aiki makamancin wannan ya taso.
Tun da farko da yake gabatar da jawabinsa yayin mika wannan rahoto, Shugaban Kwamitin Mallam Abubakar Rabo Abdulkarim, bayyana rashin gamsuwarsu ya yi game da yadda ayyukan Hisbah ke gudana a kananan hukumomin yayin da suka bukaci hukumar Hisbah ta jiha da ta gaggauta daukar matakin magance wannan matsala domin cigaban ayyukan Hukumar a duk fadin jihar Kano da ma kasa baki daya.
Daga nan kuma sai ya mika godiyarsu ga Hukumar ta Hisbah bisa ga wannan dama da ta basu na gudanar da wannan aiki mai dimbin lada a wurin Allah.