Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hisbah na shirin kara inganta ayyukanta a kananan hukumomi

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce nan bada jimawa ba zata inganta ayyukan dakarun ta dake kananan hukumomin jihar nan 44.

Babban Daraktan Hukumar Hisbah na jiha Dakta Aliyu Musa Aliyu  ne ya bayyana  hakan  kasancewar hukumar ta Hisbah a yanzu haka na kokarin ganin an kar ingantawa tare da sake yin nazari kan yadda take gudanar da ayyukan ta a daukacin   kananan hukumomin ta.

Dakta Aliyu ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar kundin rahoton yadda aka gudanar da aikin tantance dakarun Hisbah na kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Haka kuma ya bayyana rashin jin dadinsa game da yadda ayyukan Hisbah ke gudana a wasu daga cikin kananan hukumomi, inda ya ci alwashin cewa, za su hada kai da ma’aikatar kula da kananan hukumomi da kuma shugabannin kananan hukumomin domin ganin cewa al’amura sun dai-daita tun daga yadda za’a bi wajen dauka ko maye gurbin dakatar da duk wani dan Hisbah da za’a yi.idan yayi laifi ko kuma ya bar aiki.

Jami’an Hisba sun cafke mata masu zaman kansu

Yadda hukumar Hisbah ta sauke ‘yan kwamitin gudanarwarta

Hisbah ta cafke matashi kan yunkurin haikewa budurwar abokinsa

Har Ila yau, Dr.Aliyu Musa ya yabawa  kwamitin bisa yadda suka gudanar da ayyukansu tare da tabbatar musu da cewa za su ci gaba da tuntubar su a duk lokacin da wani aiki makamancin wannan ya taso.

Tun da farko da yake gabatar da jawabinsa yayin mika wannan rahoto, Shugaban Kwamitin Mallam Abubakar Rabo Abdulkarim, bayyana rashin gamsuwarsu ya yi game da yadda ayyukan Hisbah ke gudana a kananan hukumomin yayin da suka bukaci hukumar Hisbah ta jiha da ta gaggauta daukar matakin magance wannan matsala domin cigaban ayyukan Hukumar a duk fadin jihar Kano da ma kasa baki daya.

Daga nan kuma sai ya mika godiyarsu ga Hukumar ta Hisbah bisa ga wannan dama da ta basu na gudanar da wannan aiki mai dimbin lada a wurin Allah.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!