Labarai
Hisbah ta cafke mutanen da ake yunkurin yin safararsu zuwa kasashen Ketare

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta samu nasarar kama wasu mutane da ake zarginsu da yin safarar wasu Mata domin kai su kasashen ketare domin yin aikatau ko kuma wasu ayyuka na daban.
Mataimakin babban kwamandan hukumar Dakta Mujahiddin Aminuddin, ne ya bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ya aiko wa Freedom Radio.
Dakta Mujahiddin Aminuddin, ya kuma ce, mutanen su goma 12 dukkansu mata da suka fito daga jihohin Kano da Katsina da Maiduhuri da Jigawa da kuma jihar Zamfara.
You must be logged in to post a comment Login