Labarai
Hukumar binciken hadurra ta ƙasa (NSIB) ta fara bincike kan hatsarin jirgin ƙasan da ya auku a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Hukumar Binciken Hadurra ta Ƙasa (NSIB) ta fara bincike kan hatsarin jirgin ƙasan da ya auku da safiyar yau Talata a kan hanyar Kaduna bayan da hukumar ta ce mutane shida ne suka samu raunuka, amma babu wanda ya mutu.
Daraktar yaɗa labarai ta NSIB, Bimbo Olawumi Oladeji, ta bayyana cewa za a gudanar da bincike mai zurfi don gano musabbabin lamarin tare da fitar da shawarwari da za su hana faruwar irin wannan a nan gaba. Ta kuma ce za a ci gaba da sanar da jama’a ci gaban binciken.
NSIB ta jaddada cewa tana da niyyar tabbatar da tsaro da ingancin harkokin sufuri a ƙasar nan, ta hanyar gudanar da bincike na gaskiya.
You must be logged in to post a comment Login