Connect with us

Kasuwanci

Hukumar bunkasa harkokin Sikari ta hada kai da EFCC don magance lalata tattalin arziki

Published

on

Shugaban hukumar bunkasa harkokin Sikari ta kasa NSDC Mista Zacch Adedeji, ya bukaci Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da ta magance tabarbarewar tattalin arziki da sauran munanan ayyuka da bangaren.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, Adedeji bayyana EFCC a matsayin wadda ya kamata su hada gwiwa don tabbatar da ganin cewa Najeriya na iya samarwa kanta da isasshen Sikarin da take bukata.

Adedeji ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai wa Shugaban hukumar ta EFCC Abdulrashi Bawa a Abuja.

Bawa ya ce, EFCC a shirye ta ke a koda yaushe wajen bayar da gudunmowa ga hukumomin gwamnati don gudanar da ayyukan su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!