Connect with us

Kiwon Lafiya

Hukumar EFCC ta kama tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir David

Published

on

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta kama tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal.

Mukaddashin shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar Sammin Amadin ya tabbatar da faruwar lamarin a daren jiya, yana mai cewar, hukumar za ta ci gaba da rike-shi a ofishinta har sai ya kammala tattaunawa da masu bincike.

A cewar sa hukumar ta kama Babachir David Lawal ne game da zargin yin ba daidai ba a cikin shirin sake tsugunar da al’ummar yankin arewa maso gabas da rikicin Boko-Haram ya daidaita.

Rahotanni sun bayyana cewa Babachir David Lawal ya isa ofishin hukumar ne da misalin karfe goma sha daya na safiyar jiya.

 

Tun da fari dai majalisar Dattawa ce ta zargi tsohon sakataren gwamnatin tarayyar kan zargin almundahana a wata kwangilar naira miliyan dari biyu da ashirin domin cire ciyawa da kuma samar da filaye mai girmar hekta dari da sha biyar a jihar Yobe.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,340 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!