Kasuwanci
Hukumar FCCPC ta rufe shaguna da rumbunan ajiye kaya bisa zargin tauye Mudu

Hukumar kula da gasa da kare hakkin masu siyan kayayyaki ta tarayya FCCPC, ta kulle wasu shaguna da kuma manyan rumbunan adana kaya wadanda ke makare da kayyakin yadika da shaddoji.
A cewar hukumar ta na zargin cewa, an tauye mudu a kayan, kuma ana sayar wa mutane ba tare da sun sani ba, inda hakan ya saba da dokar hukumar ta shekarar 2018.
Hukumar ta kama kayan ne yayin samamen da ta kai yau laraba a wasu daga cikin sassan birnin Kano da suka hadar da Titin Ibrahim Taiwo da Gandun Albasa da Sharada da Nassarawa GRA da ma wasu yankuna.
Da ya ke yi wa manema labarai karin haske kan kamen, lauyan hukumar mai kula da ayyukanta a shiyyar Arewa maso Yammacin kasar nan Barista Jamilu Muhammed, ya ce, sun samu rahoton tauye mudu ne inda kuma suka kaddamar da bincike don tabbatar da zargin bayan da suka kulle wasu manyan rumbunan adana kayayyaki da suke zargin awon kayan bai cika ba.
Haka kuma ya kara da cewa, sun gayyaci masu kayan da su bayyana a ofishin hukumar na nan Kano domin gudanar da bincike tare da daukar mataki na gaba.
Wakiliyarmu ummulkhairi Rabi’u Yusuf, ta ruwaito cewa, hukumar ta kula da gasa da kare hakkin masu siyan kayayyaki ta tarayya FCCPC, ta sha alwashin ci gaba dasanya ido a kan masu gurabatawa ko kuma sayar da kaya marasa inganci, ko kuma wadanda aka tauye mudu.
You must be logged in to post a comment Login