Kasuwanci
Hukumar FCCPC ta yi taron faɗakar da jama’a kan gurɓatattun Kaya

Hukumar Kula da gasa da kare haƙƙin masu sayen kayayyaki ta Tarayya FCCPC, ta gargaɗi masu gurɓata Kayan abinci tare da sayar da su da su guji yin hakan ko kuma su fuskanci hukuncin gurfanarwa a gaban kotu.
Shugaban hukumar na ƙasa Mista Tunji Bello, ne ya yi wannan gargaɗi a yau Talata yayin taron masu ruwa da tsaki na wayar kan jama’a dangane da illolin tu’ammali da ƴaƴan Itatuwa da aka Nika da gurɓataccent Manja da kuma gurɓataccen Nama.
Shugaban, wanda ya samu wakilcin Daraktar sashen kula da ingancin kayayyaki ta hukunta Dakta Nkechi Mbah, ta kuma bayyana cewa akwai cutuka masu yawa da ake kamuwa da su sakamakon amfani da irin waɗannan abubuwan da aka gurɓata.
Da ya ke ganawa da manema labarai, Daraktan sashen wayar da kan masu sayen kayayyaki na hukumar ta FCCPC, Alhaji Yahaya Garba Kudan, ya bayyana cewa, hukumar za ta gurfanar da duk wanda ta samu ya na gurɓata kaya tare da sayar da su domin daƙile cutar da mutane da suke yi.
Da ya ke gabatar da muƙala yayin taron babban jami’i a ma’aikatar lafiya ta jihar Kano Umar Adamu Riruwai, ya ce, yin irin wannan ha’inci na gurɓata kayyakin masarufi abu ne da ke cutar da lafiyar jiki.
Haka kuma ya ƙara da cewa, “Ita gurɓatar kayan masarufi iri biyu ce, na farko akwai yadda ƴan kasuwa suke gurɓata Kaya suna sane domin samun riba Mai yawa kamar haɗa Zuma da Sukari ko dandaƙa Alli a haɗa shi da Fulawa ko kuma haɗa Manja da wasu sinadarai domin ya ƙara yawa da dai sauransu.”
“Haka kuma akwai gurɓatar kaya sakamakon rashin tsafta ko kuma ingancin wajen da aka ajiye su ko kuma shi mai sarrafa kayan, don haka ya kamata a kiyaye saboda akwai sinadari ko kuma abubuwan da ke cutar da lafiyar mutane.”
Taron dai, ya samu halartar shugabanni da mambobin ƙungiyoyin ƴan kasuwa da dama da suka hada da Dawanau da Singa da Galadima da kasuwa Muhammadu Abubakar Rimi Watau Sabon Gari da sauransu.
You must be logged in to post a comment Login