Kasuwanci
Hukumar FCCPC ta yi taron ganawa da yan kasuwar Dawanau

Hukumar kula da Gasa da kare haƙƙin masu sayen kayayyaki ta ƙasa FCCPC, ta ja hankalin yan kasuwar kayan Hatsi ta Dawanau da ke nan Kano da su tabbatar da cewa suna sayar wa da mutane kayayyaki masu inganci domin kauce wa yaduwar cutuka.
Shugaban hukumar na ƙasa Tunji Bello, ne ya yi wannan jan hankali yayin taron ganawa da ƴan kasuwa yau Laraba.
Shugaban wanda ya samu wakilcin Babbar jami’a a hukumar Burget Etim, ya ƙara da cewa sun ɗauki matakin zagaya wa kasuwanni tare da ganawa da ƴan kasuwa ne domin faɗakar da su kan yadda za su riƙa gudanar da kasuwancinsu yadda ya dace, inda ta ce, a baya-bayan nan sun kulle wasu shaguna da ke sayar da kayan abinci marasa inganci a Abuja.
Ta ce, “A watanni biyu da suka gabata, tawagar jam’ianmu sun rufe wasu shaguna a kasuwar Utako da da ke Abuja bayan da aka gano cewa suna sauya wa Shinkafa maras inganci buhuna inda suke nuna cewa shinkafar kasar waje ce”.
“Haka kuma, mun kirkiri tawagar kwamitin kar ta kwana masu aikin sanya ido domin dakile masu yin haramrtaccen kasuwanci ta hanyar sayar da kaya marasa inganci”, inji Burget Etim.
Ta kara da cewa, “Muna sanar da ku cewa, tawagarmu ta jami’an sanya ido kan yaki da gurbatattu da jabun kayayyaki za ta ziyarci kano kwanan nan domin gudanar da ayyuka”.
A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar Ci gaban Kasuwar ta Dawanau Alhaji Muttaqa Isa, ya bayyana cewa suna yin iyakar ƙoƙarinsu wajen tabbatar da cewa ƴan kasuwar na sayar da kaya masu inganci kuma cikin sauƙi.
Taron dai ya samu halartar da dama daga cikin shugabannin kungiyoyin ‘yan kasuwar ta Dawanau.
You must be logged in to post a comment Login