Connect with us

Labarai

Hukumar Hisbah ta kama mabarata anan Kano

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu mutum 10 da ake zargin mabarata ne tun a watan Satumbar da ya kare bayan da aka yi zargin cewar sun take dokokin hukumar na yin bara akan Titunan jihar nan.

Kakakin hukumar ta Hisba Lawan Ibrahim ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

A cewar sa wadanda ake zargin sun hada da maza 3 da mata 7.

An dai kama wadanda ake zargin da yin barar a tituna daban-daban a wani samame da hukumar ta gudanar a cikin birnin Kano.

Haka zalika  an kama mabaratan ne akan Titunan da suka hada da Railway da State Road da dai sauran su.

Sai dai kakakin hukumar ta Hisbah ya ce bayan an tantance su daga bisani an sake su, da aka gano cewar sababbi ne wajen yin barar.

Rahotanni sun bayyana cewar an sami ragowar mabarata akan tituna tun bayan da hukumar ta Hisbah ta kaddamar da samame tare da kama su, don hana masu yin bara a jihar Kano

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,149 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!