Connect with us

Labarai

Matawalle zai gana da fulani kan mutuwar sojoji 9

Published

on

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya ce, zai gana da shugabannin makiyaya Fulani sakamakon harin da aka kai kauyen Sunke da ke karamar hukumar Anka, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji tara hadi da raunata wasu da dama.

Mataimaki na musammam ga gwamnar Jihar Zamfara Abubkar Daura, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Gusau babban Birin Jihar.

Ko da yake, gwamnar Jihar bai bayyana ranar da zai gana da su ba, amma yace zaman zai haifar da da-mai-ido.

A harin dai, sojoji tara ne suka mutu wasu da dama suka samu raunuka, gwamnatin Jihar Zamfara dai na zargin cewa, maharan sun fito ne daga Jihar Niger ba ‘yan asalin Jihar Zamfara ba ne.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, wannna harin shi ne harin farko da ‘yan-tada-kayar- baya suka kai tun bayan da ya gana da su daga lokacin da yau karagal mulki.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,845 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!