Connect with us

Labarai

Hukumar ICPC na shirinta gurfanar da Nasir El-Rufai

Published

on

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta sanar da shirinta na gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban kotu a yau Talata 24 ga Maris.

 

Hukumar ta ce za ta gurfanar da shi tare da wani Joel Adoga a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna.

 

A cewar sanarwar da ICPC ta fitar a ranar Litinin, ƙarar da ake yi wa El-Rufai ta ƙunshi tuhume-tuhumen da suka hada da karkatar da kadarorin gwamnati da mallakar kadarorin jama’a ba bisa ƙa’ida ba, da kuma halsata kuɗin haram. Hukumar ta ce an shigar da karar ne domin a bi diddigin zargin da ake yi.

 

Haka kuma, ICPC ta bayyana cewa akwai wata ƙara ta daban da aka shigar a Babbar Kotun Jihar wadda ta shafi El-Rufai da wani Amadu Sule.

 

A cikin wannan ƙarar, ana zarginsu da amfani da mukami ba daidai ba da damfara, yunƙurin aikata damfara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!