Labarai
Hukumar ilimin bai daya ta Jigawa ta amince da sauke sakatarorin ilimi 27

Hukumar ilimin bai daya ta Jihar jigawa ta amince da sauke sakatarorin ilimi na jihar su 27.
Shugaban hukumar Farfesa Haruna Musa ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.
Ya ce, yanzu haka hukumar ta bude shafin intanet ga wadanda suka cancanci hawa waɗannan mukami.
Farfesa Haruna Musa ya kuma ce, su ma wadanda ke kan mukamin za su iya sake neman wannan mukami.
You must be logged in to post a comment Login