Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar INEC ta ce zaben gwamna na jihar Kano bai kammala ba

Published

on

Hukumar zabe ta kasa a nan Kano ta sanar da sakamakon gwamnan jihar Kano a matsayin wanda bai kammala ba.

A cikin daren jiya ne dai baturen zaben jihar Kano Farfesa Bello Shehu ya sanar da sakamakon zaben a matsayin wanda bai kammalaba.

A cewar farfesan ya ayyana zaben ne a matsayin wanda bai kammala, saboda adadin kuri’un da aka soke sun fi wadanda aka ci zaben da su yawa .

Da ya ke sanar da sakamakon zaben farfesan ya ce Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u miliyan daya da dubu goma sha hudu da dari hudu da saba’in da hudu, inda kuma Abdullahi Umar Ganduje ya samu kuri’u dubu dari tara da tamanin da bakwai da dari takwas da sha tara.

Yace adadin kuri’un da aka soke a  kananan hukumomi 22 ciki har da mazabar Gama ya kai kuri’u dubu dari da arba’in da daya da dari shida da casa’in da hudu. A don haka ne baturen zaben ya ce bisa tsarin doka dole ne a ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!