Kiwon Lafiya
Hukumar INEC ta yiwa yan jihar Filato 2,454,200 da za su kada kuri’a a zaben badi
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, dake jihar Filato, ta ce ta yi wa mutane Miliyan biyu da dubu dari hudu da hamsin da hudu da dari biyu ‘yan asalin jihar rijista da za su kada kuri’a a babban zaben badi.
Shugaban sashen wayar da kan jama’a na hukumar dake jihar Mr Osaretin Imahiyereobo, ne ya bayyana hakan jiya Talata a birnin Jos din jihar ta Filato.
Hukumar ta INEC ta kuma bayyana cewa alkaluman wadanda suka yi rajistar zaben a wannan karo, sun dara na wadanda suka yi rajistar a kakar zaben da ya gabata na shekarar 2015 da mutum miliyan 2 da dubu 3 da arba’in da shida suka yanki rajistar.
Mr Osaretin Imahiyereobo, ya kuma ce nan ba da jimawa ba hukumar za ta fitar da rukunin na biyu na rajistar ta din-din-din na mutum dubu dari 3 da ashirin da 6 da dari takwas da tamanin da 9 inda rajistar al’ummar jihar dubu dari hudu da hamsin da 1 da 154 wadanda suka yi rajistar tsakanin watan Afrilun shekarar 2017 zuwa 31 ga Agustan bana ta kammala.
Shugaban sashen wayar da kan jama’ar na hukumar INEC ya kuma yi kira ga wadanda suka yi rajistar ba su karba ba, da su garzaya ofisoshin hukumar da ke kananan hukumomi don karbar rajistar su.