Labarai
Hukumar jindadin alhazan jihar Bauchi ta kara wa’adin biyan kudaden aikin Hajji
Hukumar jindadin Alhazan Jihar Bauchi ta ce, ta kara wa’adin biyan kudaden aikin Hajjin bana zuwa Talatin ga watan Afrilun da muke ciki.
Shugaban hukumar Alhaji Magaji Abdullahi, wanda ya samu wakilcin Daraktan gudanarwa na hukumar Alhaji kasimu Danlami Shall ne, ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Ofishinsa.
Alhaji Kasimu Danlami Shall, ya kara da cewa, karin wa’adin ya zo ne sakamakon koken da al’ummar Jihar suka yi na bukatar kara musu wa’adin don samun damar biya.
Ya kuma ce, hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ce ta bata umarnin kara wa’adin.
AlhajI Kasimu ya kuma shawarci maniyyatan Jihar su biya Naira Miliyan daya da dubu dari biyar kafin wa’adin da hukumar ta bayar ya kare.