Labarai
Hukumar kula da da’ar ma’aikata zata fara tantance kadarorin gwamnan jihar Oyo
Hukumar kula da da’ar ma’aikata (CCB), ta ce, za ta fara bibiya tare da tantance kadarorin da gwamnan jihar Oyo, Seyi makinde ya gabatar gareta, domin tabbatar da gaskiyar ikirarin sa, na mallakar kadarar da ta kai sama da naira biliyan arba’in da takwas.
Babban jami’in hukumar a jihar Oyo, Mr. Bisi Atolagbe ne ya bayyana haka a birnin Badun, yayin wani taron da Shugabannin hukumar na yankin kudu maso yammacin kasar nan su ka gudanar.
Ya ce, a makwanni kadan da suka wuce ne, ofishin hukumar da ke jihar Oyo ya mika da bayanan kadarorin gwamnan zuwa shalkwatarsu da ke Abuja don nazartar sa.
Sai dai Mr. Bisi Atolagbe, ya ce, za a dau tsawon lokaci ana gudanar da aikin tantancewar domn tabbatar da cewa, an yi komai bisa tsarin doka.
A watan Yuni ne dai gwamnan jihar na Oyo, Seyi Makinde, ya sanar da cewa, ya mallaki kadarorin da darajarsu su ka kai sama da naira biliyan arba’in da takwas.