Kaduna
Hukumar kula da jirgin kasa ta ce a mako mai zuwa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna zai koma aiki

Hukumar kula da zirga zirgan jirgen kasa ta kasar nan, ta ce, ta kammala gyare-gyare layin dogon Abuja- zuwa Kaduna.
A cikin sanarwar da mai magana da yawunta Callistus Unyimadu ya fitar, hukumar ta ce jirgin zai koma aikin jigilar fasinja a hanyar a mako zuwa.
Sanarwa ta ce hukumar ta yi aiki tukuru wajen tabbatar da kammala gyare-gyaren cikin tsanaki.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana asalin ranar da jirgin zai koma aiki ba.
Idan dai za iya tunawa, a ranar 26 ga watan Agusta ne dai jirgin ya tuntsure, inda wasu mutane da dama suka samu raunuka, lamarin da ya sa aka dakatar da aikin jirgin domin a yi gyara.
You must be logged in to post a comment Login