Connect with us

Labarai

Hukumar Kwastam ta kama hodar Iblis ta Naira Biliyan 1

Published

on

Hukumar hana fasa kauri ta kasa ta kama kunshi 22 na hodar iblis mai nauyin kilo 25 da darajarta ta kai Naira biliyan daya.

Shugaban hukumar, Adewale Adeniyi, ya bayyana cewa jami’an rundunar Seme sun tare wata mota kirar Toyota Highlander dauke da kunshin hodar a yankin Badagry-Seme da misalin karfe 3:00 na asubahin ranar 10 ga Fabrairu, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri. An kama mutum daya da ake zargi da hannu a safarar.

 

Daga bisani, an mika hodar iblis din da motar da aka yi amfani da ita da kuma wanda ake zargi ga Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLE domin zurfafa bincike.

 

Kwamandan hukumar a Legas ya ce darajar hodar ta kai Naira miliyan 40 kan kowanne kilo, yana mai jaddada cewa za a hukunta duk masu hannu a lamarin.

 

A bangaren gyaran aiki kuwa, shugaban Hukumar hana fasa kauri ya ce za a fara aiwatar da tsarin “One-Stop-Shop” da kuma matakin farko na aiki ba takarda kafin karshen zangon biyu na shekarar nan, domin rage jinkiri, kara saurin fitar da kaya da inganta harkokin kasuwanci a fadin kasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!