Labarai
Hukumar Kwastam za ta fara gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi kan jami’anta

Hukumar hana Fasa Kwauri ta Najeriya Kwastam, ta ce za ta mayar da yin gwajin tu’ammali da miyagun ƙwayoyi a matsayin wajibi ga dukkan sabbin jami’ai da kuma ma’aikatan da ke yi aiki a hukumar domin tabbatar da ingancin ɗabi’a da tabbatar da tsaro.
Shugaban hukumar na kasa Adewale Adeniyi ne ya sanar da daukar wannan matakin a wajen bikin rufe taron hukumar na bana da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Ya kuma bayyana cewa gwajin muhimmin ɓangare ne na tsarin ɗaukar ma’aikatan hukumar na shekara.
Haka kuma, ya kara da cewa, daukar matakin na da nufin daukar jami’ai masu halaye nagari, ba masu maimakon masu tu’ammali da miyagun ƙwayoyi.
Adeniyi ya kuma bayyana cewa, duk da matakin ya fi karkata ga sabbin ma’aikata, zai shafi dukkan ma’aikata a shalkwatar hukumar da sassa da kuma rundunonin hukumar, domin ganin cewa, jami’ansu ba su da alaƙa da shay
e-shaye.
You must be logged in to post a comment Login