Connect with us

Labarai

Hukumar NAFDAC ta kwace kwayoyi da jabun magunguna na Naira biliyan uku a Kano.

Published

on

Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta NAFDAC ta  kwace jabun kayayyaki da abinci da yakai kimanin Naira biliyan 3 a Kano.

Shugaban hukumar ta NAFDAC mai kula da jahar Kano Muhammad Shaba ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da hantsi a ranar litinin din makon da muke ciki.

Muhammad Shaba yace tun zuwan sa Kano a shekarar 2018 yayi kokari wajen hada kai da hukumomin tsaro da ya hada da hukumar hana fasa  kwauri ta Custom da NDLEA wajen ganin an magance matsalar ta amfani da miyagun kwayoyin da jabun kayyyaki.

Muhammad Shaba yace hukumar ta NAFDAC tana bibiyar yadda kamfanin hada ruwa na leda dake tafiyar da hada ruwan ba tare da jamaa sun cutu ba.

Yace kuma sun hana gudanar da sanaar kamfanin na ruwa kusa da kwatami.

Yace a yanzu akwai sharioi dake gaban babbar kotun tarayya da ta shafi harkokin sha da fataucin miyagun kwayoyi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,069 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!