Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

An zargi jami’an SARS da  sanadiyyar mutuwar wani matashi

Published

on

Yan uwan wani matashi mai suna Baffa a nan Kano, sun koka bisa zargin da suke yiwa jami’an ‘yan sanda na sashen da ke yaki da ‘yan fashi da makami watau SARS na yi sanadiyyar mutuwarsa.

Yan uwan marigayin sun bayyana cewa, wani magidanci ne ya gayyaci Baffan da cewa ya taya shi kwashe kaya a wani gida, sai dai ashe kayan na maigidansa ne kuma ya debi kayan ne da niyyar sata wanda matashin bai san da hakan ba.

Sai dai bayan an kwashe kayan ne sai jami’an sashen na SARS suka kama Baffan tare da tsare shi a tsawon lokaci suna gana masa azaba, ba tare da sun gurfanar da shi a gaban kotu ba.

Sun kara da cewa bayan ya kwashe tsawon kwanaki  suna gana masa azaba sai aka kira su da su zo su dauki gawarsa a sashen na SARS, kamar yadda wani dan uwansa ya bayyana.

Yan uwan marigayin sun bukaci kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano da shiga lamarin tare da bi musu hakkin dan uwan na su.

Sai dai ko da Freedom Radio ta tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bakin kakakinta DSP Abdullahi Haruna Kiyawa,  ya ce zai bincika lamarin sannan ya yi bayani, amma kawo yanzu bamu ji daga gareshi ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!