Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Hukumar NAHCON za ta hada hannu da hukumar NAPTIP wajen magance safarar bil’adama

Published

on

Hukumar lura da aikin hajji ta Najeriya NAHCON ta ce zata hada hannu da hukumar dake yaki da safarar bil’adama ta kasa NAPTIP don magance matsalar safarar bil’adama.

Shugabar sashen yada labaran hukumar NAHCON Hajiya Fatima Mustapha, ce ta bayyana haka a yau Juma’a.

Ta kuma kara da cewa hukumar ta NAHCON karkashin jagorancin Alhaji Abdullahi Muhammad ne ya bayyana hakan lokacin da hukumar ke karbar bakuncin hukumar NAPTIP a Abuja.

Fatima ta kuma bayyana cewar shugaban hukumar na yin kira ga dukkanin hukumomin da abin ya shafa da su hada hannu guri guda don magance matsalar safarar mutane, inda ya ce safarar mutane babbar matsala ce da ke addabar al’ummar kasar nan.

Sannan kuma sai ya yi kira ga gwamnati da ta samar da wani yanayi da hukumomin biyu zasu rika gudanar da ayyukan su tare wajen yaki da safarar mutane, musamman masu kin dawo wa daga kasar Saudiyya bayan kammala aikin hajji.

Da ta ke jawabi shugabar hukumar yaki da safarar Bil’adama ta kasa Julie Okali-Donli ta yabawa hukumar ta jin dadin alhazai bisa yadda take gudanar da ayyukan ta.

Ta kuma ce hukumar a shirye ta ke ta hada hannu da hukumar NAHCON don dakatar da ta’adar safarar mutane da sauran laifuffuka.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!