Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bukola Saraki ya yi Allah-wadai da harin da yan fashi suka kai a karamar hukuma Offa

Published

on

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki ya yi Allah-wadai da harin da wasu da ake zargin yan fashi ne suka kai kan wasu bankuna a yankin karamar hukuma Offa dake jihar Kwara Lamarin da yayin sanadiyyar mutuwar Mutane kimanin 30.

Bukola Saraki wanda dan Asalin jihar ta Kwara ne ya bayyana harin a matsayin Abin takaici da tatar da hankali ga al’ummar karamar hukumar ta Offa da kuma jihar ta Kwara baki daya.

Ya kuma kara da cewa a jiya ya zanta da Gwamnan jihar Abdul Fatah Ahmed don mika ta’aziyyar sa gare shi, inda kuma ya tabbatar da cewa jami’an tsaro za su tabbatar da kamo masu hannu kan wannan al’amari tare da hukunta su.

Sannan kuma yayi kira ga al’ummar jihar da su baiwa jami’an tsaro hadin kai wajen tabbatar da bincike da kuma gurfanar da masu hannu kan wannan aika-aika da kuma hada hannu waje guda don tabbatar da tsaro a jihar.

Daga nan kuma sai ya yi fatan samun rahamar sa ga wadanda suka mutu tare da yin ta’aziyya ga iyalan su.bb

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!