Labarai
Hukumar NiMet ta fitar da sabon hasashen yanayi

Hukumar lura da yanayi ta kasa NiMet, ta ce za’a samu saukar ruwan sama da tsawa na kwanaki uku daga yau Litinin zuwa Laraba a sassan jihohin Kano da Jigawa da Zamfara sai Kaduna da Bauchi da Yobe da kuma jihar Katsina.
Haka kuma, hukumar ta ce, za a samu yayyafi da yammacin wadan nan ranaku a jihohin Jigawa da Zamfara da Kano da Kaduna da Bauchi da Yobe da Katsina da Kebbi da kuma Adamawa da Taraba.
Hasashen ya kuma bayyana cewa za a iya samun saukar ruwan a kowanne lokaci cikin wadan nan ranaku a jihohin Bauchi da Jigawa sai Katsina da Kaduna da kuma jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login