Labarai
Hukumar NiMet ta fitar da sabon hasashen yanayi

Hukumar Kula da yanayi ta kasa NiMet ta yi hasashen cewa za’a samu yanayin kwallewar Rana daga yau Litinin zuwa Laraba a wasu sassan kasar nan.
A cewar rahotan yanayin da NiMet din ta fitar a jiya Lahadi a birnin tarayya Abuja ta ce yankin Arewa zai kasance da mai zafi tare da gajumare na tsawan kwanaku Uku.
A kudancin Najeriya kuwa, ana sa ran samun tsawa da ruwan sama kadan kadan a wasu sassan jihohin Bayelsa da Rivers Akwa Ibom da Cross River
A yankunan Arewa ta tsakiya kuwa suma zasu fuskanci hasken Rana mai dauke kura da Kuma hazo.
Hukumar ta yi gargadin cewa kura da iska tana yawo a yankin Arewa ta tsakiya inda ta shawarci jama’a su dauki matakan kariya musamman masu fama da cututtukan numfashi irin su Asma.
You must be logged in to post a comment Login