Labarai
Hukumar NiMet ta yi hasashen samun mamakon Ruwa da Tsawa

Hukumar dake lura da hasashen masana yanayi ta kasa NiMet ta yi hasashen cewar za a samu ruwan sama mai karfi tare da Tsawa na tsawon kwanaki uku daga yau Litinin a sassan kasar nan.
NiMet ta bayyana hasashen nata ne cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Internet.
Sanarwar ta kuma ce, za a samu yanayin Chida da ruwan sama a jihohin Kano da Bauchi da Taraba da Kaduna da Kebbi da kuma Katsina.
Haka kuma, ta ce za a samu ruwan sama da tsawa a kwanaki ukun a jihohin Zamfara da Adamawa da Kebbi da Taraba da kuma Kaduna, sai Kogi da Niger da Benue da Plateau da Nasarawa da kuma birnin tarayya Abuja.
Yayin da jihohin kudu da suka hadar da Lagos da Ogun da Ondo da Akwa Ibom da Cross River da Rivers da Delta da kuma Bayelsa za a samu saukar ruwan sama mai karfi.
You must be logged in to post a comment Login