Labarai
Hukumar NiMet ta yi hasashen samun mamakon Ruwan sama da Guguwa

Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya NiMet ta yi hasashen samun mamakon Ruwan sama da Guguwa mai karfi daga ranar Litinin Zuwa Laraba a fadin Ƙasa.
Ta cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja, NiMet ta bayyana cewa ana sa ran samun iska hade da guguwa hadi da ruwan sama da safe a wasu sassan jihohin Sokoto, Kebbi, Zamfara, Taraba, Adamawa da Kaduna da ke yankin Arewacin kasar.
Hukumar ta ce ana sa ran guguwar iska mai ɗauke da ruwa da yamma ko da rana a wasu sassan Adamawa, Taraba, Borno, Jigawa, Yobe, Kano, Katsina, Gombe, Sokoto, Kebbi, Zamfara da Kaduna.
Ta cikin rahoton Nimet, ce za a iya samun guguwa da ruwan sama da safe a wasu sassan jihohin Neja, Filato da babban birnin tarayya FCT, yayin da sauran sassan yankin zai kasance cikin rana da gajimare kaɗan.
A karshe hukumar ta NIMET ta shawarci direbobi da su kula da tuki domin akwai hatsari a irin wannan yanayi.
You must be logged in to post a comment Login