Labarai
Hukumar NRC ta fitar da rahoton hatsarin layin dogo na Abuja zuwa Kaduna

Hukumar kula da sifurin jiragen Ƙasa ta Najeriya NRC, ta fitar da rahoton bincike kan hatsarin da ya faru a layin dogo na Abuja zuwa Kaduna.
Ta cikin wata sanarwa da shugaban hukumar, Kayode Opeifa ya sa wa hannu, ya ce binciken ya gano cewa gudu fiye da kima da kuma kuskuren amfani da na’urar birki na gaggawa ne suka haddasa hatsarin.
Ya ce kuskuren ɗan adam ne ya fi taka rawa a cikin lamarin, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da shawarwarin da kwamitin binciken ya bayar domin kaucewa maimaituwar irin haka a gaba.
Idan za a iya tunawa, a ranar 26 ga watan Agusta, jirgin ya yi hatsari da fasinjoji 618 a ciki, inda mutane 21 suka samu raunuka.
You must be logged in to post a comment Login