Connect with us

Labarai

ICPC: zata rinka bibiyar kudaden da aka ware don yakar Covid-19

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta kafa wani kwamiti da zai ke bibiyar kudadan da aka ware domin yaki da cutar Corona.

Mai Magana da yawun hukumar Mrs Rasheedat Okoduwa ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar a birnin tarayya Abuja.

Okuduwa tace gamayyar jamian ta hukumar ICPC zata saka ido game da yadda zaa rika raba kudaden tallafin cutar ta Corona da sauran taimakon da zaa bayar da kuma abubuwan da aka karba daga guraran al’umma domin yaki da cutar.

Okuduwa ta kuma jaddada matsayar hukumar ta ICPC na kira ga duk masu ruwa da tsaki a harkar ta cutar covid 19 da su nesanta kansu daga duk wani abu da zai sa su fada cikin ayyukan cin hanci da rashawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,751 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!