Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ina Aisha Buhari take?, fadar shugaban kasa ta yi martani

Published

on

Fadar shugaban kasa ta maida martani kan zargin da wasu ke yi cewa Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi yaji.

A cewar fadar shugaban kasar Aisha Buhari na da ‘yancin tafiya duk in da take son zuwa, kuma bata yi rikici da kowa ba a fadar shugaban kasar dake Abuja.

Bayanin haka ya fito ne ta bakin mai Magana da yawun ta Suleman Haruna ‘’cewa watannin 2 da ba’a ganin fuskar uwargidan shugaban kasar, ba yana nufin cewar babu fahimtar juna a tsakanin ta da maigidan ta ba ko kuma wasu jiga-jigan gwamnati mai ci’’, a’a illa kawai wasu ne ke kitsa labarun karya don tada fitina’’

Rahotanni sun bayyana cewar fadar shugaban ta tabbatar da cewar uwargidan shugaban kasar ba ta kasar nan, amma kuma ba yaji tayi ba,illa kawai kowannne dan adam na da uziri kamar kowa a don haka babu zancen cewa tana da ‘yar tsama da shugaban kasa da kuma makarraban sa.

Sai dai  idan aka gayyaci Aisha Buhari babbar mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin sha’anin mulki Dr, Hajo Sani na wakiltar ta, ciki har da taron kungiyar cigaban matan shugabannin kasa na kashashen Afrika wanda aka yi a ranar 25 ga watan nan da muke ciki karo na 74 wanda yake cikin kunshin babban zauren taron majalisar dinkin duniya da aka yi birnin New York.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!