Connect with us

Labarai

Shin Aisha Buhari tayi yaji?

Published

on

Shin Aisha Buhari tayi yaji?

Rahotannin sun bayyana cewar tun bayan kammala aikin Hajjin Bana ba’a sake ganin fuskar Uwar gidan shugaban kasa ba Hajiya Aisha Buhari ba.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa tun bayan kammala aikin Hajji Uwar gidan shugaban kasar ta ziyarci birnin Landan ana hasashen cewa kamar ta yi yaji ne, ka san cewar ta jima tana sukan irin salon mulkin shugaba Buhari.

Na baya-bayan nan dai shine furucin da tayi a lokacin da ta ziyarci jihar shugaban kasar wato jihar Katsina, inda ta bayyana takaicinta kan yadda tace ‘yan arewa na baiwa gwamnatin kuri’a amma wasu al’umma daban ne ke cin gajiyar gwamnatin.

Har ila yau wasu na ganin cewar ba’a ganin fuskokin ta a muhimman wurare tare da shugaban kasar ba, kamar taron majalisar dinkin duniya da aka kamamla kwana nan da dai sauran su.

Sai dai wasu na zargin cewar uwar gidan shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari bata jituwa da wasu daga cikin manyan kusoshin gwamantin, wanda hakan ya sanya dagantaka tayi tsami a tsakanin su har ta kai ga tayi yaji.

Ko menene gaskiyar wannan batu?

Kawo yanzu ana ta tafka mahawara a kafafan Sada zumunta kan menene dalilan da suka sanya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!